DSSC, SSC: Rundunar soji za ta dauki sabbin manyan sojoji masu yawa, ta fitar da ka'idoji da sharuda

DSSC, SSC: Rundunar soji za ta dauki sabbin manyan sojoji masu yawa, ta fitar da ka'idoji da sharuda

Rundunar sojin Najeriya (NA) ta bayyana cewa zata dauki sabbin manyan sojoji da suka kammala manyan makarantu a karkashin tsarin DSSC da SSC.

Rundunar sojin ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a shafukan ta na dandalin sada zumunta (Facebook da Twitter) a ranar Laraba, inda ta bayyana cewa ta bude shafinta na yanar gizo da za masu neman aiki zasu cike.

A cikin sanarwar, rundunar sojin ta bayyana cewa zata saurari masu neman aiki da suka cike bayansu a shafinta na yanar gizo ne kawai.

A wani labarin na Legit, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da kisan jami'an ta uku da kuma raunata wasu da dama yayin da wasu dakarun sojojin Najeriya suka bude wa tawagar 'yan sanda wuta a jihar Taraba.

A cewar rundunar 'Yan sanda, lamarin ya faru ne a kan titin Ibi zuwa Jalingo.

Felix Adojie, mataimakin sufritandan 'yan sanda ya jagoranci tawagar 'yan sandan ne domin kamo wani mutum da ake zargin shugaban masu garkuwa da mutane ne da aka ce sunan sa, Alhaji Hassan Wadume.

Sai dai, da yammacin ranar Alhamis, rundunar 'yan sanda ta aike da sakon wasu tambayoyi guda biyu ga rundunar sojin Najeriya dangane da kisan jami'anta guda uku da kuma sakin mai laifin da suka kama.

DUBA WANNAN: Okoi Obono-Obla: Buhari ya dakatar da daya daga cikin 'yan lelensa bayan 'an kai ruwa rana'

A cikin wasu gajerun sakonni da ta saki a shafinta na Tuwita, rundunar 'yan sanda ta ce, "idan har rundunar soji na ikirarin cewa sun kubutar da Alhaji Hassan Bala Wadume ne bisa tunanin cewa an yi garkuwa da shi, me yasa basu dauke shi zuwa wata bariki ko ofishin rundunar soji ba domin daukar bayanansa da kuma gudanar da sauran matakan tsaro da rundunar soji ke dauka duk lokacin da ta kubutar da wani mutum ko mutane ba?

"Me yasa suka harbi jami'an 'yan sanda duk da sun sanar da su tare da nuna musu shaidar cewar su ma'aikata ne kamar yadda kowa zai iya gani a cikin faifan bidiyon kisan 'yan sandan da yanzu haka ke yawo a kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta?"

An ruwaito cewa dakarun sojin sun kashe sufetan 'yan sanda daya da wasu masu mukamin saja biyu tare da raunatta wasu. Sun kuma kashe farar hula guda daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel