Okoi Obono-Obla: Buhari ya dakatar da daya daga cikin 'yan lelensa bayan 'an kai ruwa rana'

Okoi Obono-Obla: Buhari ya dakatar da daya daga cikin 'yan lelensa bayan 'an kai ruwa rana'

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da dakatar da Okoi Obono-Obla, shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin kwato dukiyar gwamnati daga hannun 'yan siyasa da ma'aikatan gwamnati da suka yi sama da fadinsu.

A cikin takardar da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaba Buhari ya amince da dakatar da Mista Obono-Obla tare da umartarsa ya mika kansa ga hukumar yaki da rashaw a tsakanin jami'an gwamnati (ICPC), kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa.

Buhari ya dakatar da Mista Obono-Obla ne bayan an kai ruwa rana a kan batun zarginsa da karyar takardar karatu da kuma ragowar wasu laifuka masu alaka da cin hanci.

Takardar dakatar da Mista Obono-Obla, wacce Mista Mustapha ya saka wa hannu, ta nuna cewa Mista Dayo Apata, lauyan gwamnatin tarayya, zai cigaba da jagrancin kwamitin kwato dukiyar gwamnati daga hannun masu handama da babakere.

Kazalika, takardar dakatarwar ta bayyana cewar ragowar mambobin kwamitin na nan daram a kan mukamansu, a saboda haka dakatar da Mista Obono-Obla bai shafe su ba.

Majiyar Jaridar Premium Times ta tabbatar mata da cewa Mista Mustapha ya aika wa Mista Obono-Obla sakon ko ta kwana a kan ya zo ya karbi takardar dakatar da shi daga ofis. Ba a bude ofishinsa ba da safiyar ranar Litinin har zuwa rana, lokacn da wakilin jaridar ya ziyarci ginin da ofishin ya ke.

DUBA WANNAN: Tarihin attajirin mai garkuwa da mutanen da ya haddasa rikici tsakanin 'yan sanda da sojoji

Alamun cewa akwai matsala tsakanin Mista Obon-Obla da fadar shugaban kasa sun fara fito wa ne ranar Juma'a bayan jami'an 'yan sanda sun dira ofishinsa da ke unguwar Asokoro tare da rufe shi.

Wata majiya da ke da masaniya a kan harkokin bincike ta bayyana cewa an umarci jami'an tsaro su rufe ofishin Mitsa Obono-Obla ne don kar ya samu damar kwashe wasu kaya, musamman takardu, da za a iya amfani da su wajen tuhumarsa.

Ana zarginsa da tafka almundahana a aikin da aka bashi na kwato kadarorin gwamnati daga hannun barayin gwamnati, lamarin da ya hana aikin ya yi wani tasirin kirki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel