Kaduna: El-Rufai zai gina kasuwar zamani (Mall) ta N3.9bn

Kaduna: El-Rufai zai gina kasuwar zamani (Mall) ta N3.9bn

-El-Rufai ya kaddamar da aikin gina kasuwar zamani ta N3.9bn a Kaduna

-Kamar yadda gwamnan ya fadi ana sa ran kammala aikin ginin cikin shekara daya da rabi ne

-Gwamna El-Rufai ya kaddamar da wannan aikin ranar Laraba inda ya bayyana wa yan jarida cewa aikine na hadin gwiwa tsakanin gwamnati da wani kamfani mai zaman kansa

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai a ranar Laraba ya kaddamar da aikin ginin katafariyar kasuwa ta zamani mai suna Galaxy Mall a kan zunzurutun kudi N3.9bn wadda ake sa ran kammalawa cikin watanni 18.

Gwamnan ya fadi cewa aikin hadin gwiwa ne zai gina kasuwar tsakanin gwamnati, kamfanin Amsalco wanda ke zaman kansa da kuma bankin UBA.

KU KARANTA:Ba a kai hari tashar mota ba – Gwamnatin Kogi

Da yake magana wurin bikin kaddamar da wannan aikin, El-Rufai ya ce za ayi ginin kasuwar ne a cikin fili mai girman eka hudu.

Haka zalika, idan an kammala ginin kasuwar za a fitar da hanyoyin tafiya da kafafuwa, dakunan silma uku, guraren cin abinci shida, layin shaguna 48 da kuma wurin fakin motoci sama da 360.

“ Samun irin wannan kasuwa ta zamani abu ne mai kyau ga ko wane birni. Saboda akwai ‘yancin zaben abubuwan saye kala daban-daban. Sannan kuma hanya ce ta samar da aikin yi ga mutane da dama tun daga lokacin fara gininta har zuwa karshe.

“Manoma masu saye da sayarwa, masu dauko kayan zuwa kasuwa duk zasu amfana kuma za ta bunkasa tattalin arzikinmu.” Inji Gwamnan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel