Daga karshe: Asibitin kasar India ya amince da bukatar El-Zakzaky bayan 'an kai ruwa rana'

Daga karshe: Asibitin kasar India ya amince da bukatar El-Zakzaky bayan 'an kai ruwa rana'

- Kasar India ta amince likitocin da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya amince da su su fara duba shi

- Ta farko da mahukunta kasat sun bawa Zakzaky wa'adin sa'o'i biyu ya fice daga kasar saboda ya ki amincewa likitocin da bai sani ba su duba shi

- Shugaban na IMN ya yi ikirarin cewa gwamnatin Najeriya da na Amurka suna hada makirci don kawo masa cikas wurin neman lafiya

Mahukunta Asibitin Medanta da ke New Delhi a kasar India sun amince da bukatar shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) Ibrahim El-Zakzaky, na bari ya ga liktitocin da tun farko ya zaba domin su duba shi.

A baya Sahara Reporters ta ruwaito cewa gwamnatin kasar India ta bawa El-Zakzaky wa'adin sa'o'i biyu ya fice daga kasarta saboda ya ki amincewa wasu likitocin da bai sani ba a asibitin su duba shi a ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Tsohon kwamishinan 'Yan sanda ya fadi wadanda ke daukan nauyin 'yan bindiga a Najeriya

Sai dai wani mamba hukumar kiyaye hakkin biladama a Landan da ya yi magana da majiyar Legit.ng ya bayyana cewa mahukunta asibitin na India sun amince likitocin da shugaban na IMN ya zaba tun farko su fara duba lafiyarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel