Kisan 'Yan sanda: An kama sojoji 5 da 'Yan sanda 2 a Taraba

Kisan 'Yan sanda: An kama sojoji 5 da 'Yan sanda 2 a Taraba

Kwamitin da aka kafa domin binciken mutuwan 'yan sanda 3 da sojoji suka kashe a Taraba a ranar 6 ga watan Augustan 2019 ta kama 'yan sanda biyu da ke aiki a ofishin 'yan sandan da ke Ibbi.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kama 'yan sandan ne saboda aka zarginsa tsegunta wa kasurgumin mai garkuwa da mutane Hamisu Wadume shirin da 'yan sanda ke yi na kama shi.

An ce an tafi da 'yan sandan da aka kama zuwa Abuja.

An kuma ce kwamitin ta bayar da umurnin kama sojoji biyar da suke bakin aiki a wurin da aka sojoji ke bincike a hanyar.

DUBA WANNAN: Tsohon kwamishinan 'Yan sanda ya fadi wadanda ke daukan nauyin 'yan bindiga a Najeriya

Majiyar Legit.ng ta kuma gano cewar an cire shingen jami'an tsaro da ke iyakan Wukari da karamar hukumar Ibbi.

An kuma gano an tafi gawarwarkin 'yan sanda uku da farar hula daya da aka kashe zuwa Abuja.

Majiyar ta Legit.ng ta kuma gano cewa wasu mutane 60 da ake zargin suna yi wa shugban masu garkuwa da mutanen, Hamisu Wadume aiki sun tsere.

Wadanda suka tsere din sun hada da manajan da ke kula da motoccin haya na Wadume da wasu da suka amfana da kudadensa.

A cewar majiyar, duk mutanen sun tsere ne kwanaki biyu bayan kashe jami'an 'yan sandan uku da farar hula daya.

Jami'an 'yan sanda karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan 'yan sanda (DCP) Abba Kyari sun rufe wasu gidaje da ake zargin mallakin wadanda ake zargi da garkuwa da mutane a Ibbin ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel