Shehu Sani ya goyi bayan umurnin da Buhari ya bai wa CBN kan hana shigo da abinci

Shehu Sani ya goyi bayan umurnin da Buhari ya bai wa CBN kan hana shigo da abinci

Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, ya goyi bayan umurnin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa babban bankin Najeriya (CBN) game da shigo da abinci kasar.

Sani a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, @ShehuSani, a ranar Laraba, 14 ga watan Agusta, yace umurnin da Shugaban kasar ya bayar, inda ya bukaci CBN ta daina bai wa masu shigo da abinci kudaden kasar waje “shine matakin ci gaba madaidaiciya”.

“Umurnin Shugaban kasa zuwa ga CBN da ta daina bayar da kudade kasar waje ga masu shigo da abinci shine matakin ci gaba. Zai bunkasa harkar samar da abinci a cikin gida. Abu na gaba shine mika harkar kudin noma ga bankin noma ba wai CBN ba sannan a kare manoma daga masu garkuwa da mutane,” inji shi.

A baya mun ji cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci Babban Bankin kasar da ya daina bai wa masu shigo da abinci kasar kudaden kasar waje a wani mataki na bunkasa harkar noma.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: El-Zakzaky da matarsa ba su tsira ba a asibitin Indiya – IMN

Ya ce kamata ya yi a adana kudaden da ke asusun kasar na kasashen ketare domin amfani da su wurin fadada tattalin arzikin kasar "maimakon daure wa masu shigo da abinci daga kasashen waje gindi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel