Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sace wani malamin addini a Kaduna

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sace wani malamin addini a Kaduna

Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sake sace wani fasto, Rabaran Elisha Noma na Cocin Nagarta Baptist da ke Angwan Makiri kusa da Udawa a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Hakan na faruwa ne makonni biyu bayan wasu masu garkuwa da mutane sun kashe wani faston Cocin Living Faith da ke Angwan Romi a Kaduna mai suna Jeremiah Omolewa sannan aka biya kudin fansa kafin suka sako matarsa.

'Yan bindigan kimanin su 20 ne suka afka gidan gidan faston misalin karfe 1.30 na daren ranar Laraba suka yi awon gaba da shi da dansa.

DUBA WANNAN: Tsohon kwamishinan 'Yan sanda ya fadi wadanda ke daukan nauyin 'yan bindiga a Najeriya

Amma daga baya sun sako dansa, Emmanuel Elisha bayan sun masa barazanar cewa za su halaka mahaifinsa idan bai samo wani adadin kudi ba cikin kwanaki 5.

A cewar dan faston, "Sun zo misalin karfe 1 na dare. Sun kai kimanin mutane 20 suka zo kauyen da suna ta buga kofofin mutane amma babu wanda ya bude musu. Daga nan sai suka fara afkawa gidajen mutane da karfi da yaji suna sace kayayakin mutane.

"Sun sace ni tare da mahaifi na. Amma bayan wani dan lokaci a cikin daji sun sake ni amma suka tafi da mahaifi na. Daya daga cikinsu yana sanye da kayan sojoji.

"Da za su saki ne, sunyi barazanar cewa za su kashe mahaifi na cikin kwanaki biyar duk da cewa ba su fadi adadin kudin da suke so ba.

"Ba mu sanar da 'yan sanda ba saboda a baya da hakan ya faru muka sanar da su babu abinda suka tsinana saboda babu amfani."

A halin yanzu, Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Najeriya, DSP Yakubu Sabo bai amsa sakon da aka aika masa ba kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel