Yanzu Yanzu: El-Zakzaky da matarsa ba su tsira ba a asibitin Indiya – IMN

Yanzu Yanzu: El-Zakzaky da matarsa ba su tsira ba a asibitin Indiya – IMN

Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), wacce aka fi sani da Shi’a a ranar Laraba, 14 ga watan Agusta ta koka kan cewa gwamnatin tarayya ta hana likitoci kula da shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky a kasar Indiya.

Babban sakataren kungiyar ta IMN, Abdullahi Musa, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a Abuja kan lamarin ya bayyana cewa hukumomin tsaro da suka yi wa El-Zakzaky rakiya sun bashi sa’o’i biyu ne kacal kan ya amince kula dashi kamar wani mai laifi.

Da farko mun ji cewa El-Zakzaky ya koka kan halin tsatstsauran matakan tsaro da aka sanya musu a asibitin daya tafi neman lafiya tare da matarsa a kasar Indiya, don haka ya nemi ya koma Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito Zakzaky ya bayyana haka ne cikin wani hira da yayi kuma aka nada, wanda a yanzu haka yana yawo a kafafen sadarwar zamani, inda yace jami’an tsaron Najeriya da na kasar Indiya sun hana likitocin asibitin Medanta na kasar Indiya su dubasu.

KU KARANTA KUMA: Wasu kungiyoyi na nan suna zanga-zangar neman a saki Sowore a Abuja

Daga karshe Zakzaky ya nemi a mayar dashi Najeriya don yin nazari kan halin da ake ciki, tare da duba yiwuwar zabi cikin wasu kasashe guda uku da suka nuna sha’awar amsansu, da suka hada da Maleshiya, Indoneshiya da kuma Turkiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel