Ana jita-jitar Shugaban kasa Buhari ya tsige Okoi Obono-Obla

Ana jita-jitar Shugaban kasa Buhari ya tsige Okoi Obono-Obla

Rahotanni daga jaridar Premium Times sun nuna cewa mai girma shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari, ya sauke Okoi Obono-Obla daga kujerar da ya ke kai a gwamnatinsa.

Mista Okoi Obono-Obla shi ne shugaban kwamitin da a ka kafa domin karbo kadarorin gwamnati da ke hannun mutane, kuma ya kasance Mai ba shugaban kasa shawara a game da yaki da rashawa.

Shugaban kasar ya sallami Okoi Obono-Obla bayan shekara guda a na ta faman ka-ce-na-ce game da takardun Hadimin. A na zargin Obono-Obla da amfani da takardun bogi wajen shiga makaranta.

Bincike ya nuna cewa Mista Obono-Obla ya yi wuru-wuru wajen shiga jami’ar Jos inda ya karanci ilmin shari’a. Wannan ya sa hukumar ICPC ta bada rahoto cewa ya kamata a sallame shi daga aiki.

KU KARANTA: Yadda SPIP ta tsinci Biliyoyi a cikin akawun din wasu Ma'aikatan Gwamnati

Premium Times ta ce shugaban kasar ya dauki mataki ne bayan wannan bincike da hukumar ICPC ta yi a game da Hadimin na sa. ICPC ta ce bai kamata wannan mutumi ya cigaba da rike ofis ba.

Bugu-da-kari shugaban kwamitin na SPIP ya yi ta samun matsala da mataimakin shugaban kasa inda ya rika sabawa umarnin Mai girma Yemi Osinbajo a wasu lokuta ba tare da an dauki mataki ba.

Majiyar ta bayyana cewa an nemi Okoi Obono-Obla ya ajiye mukamin na sa cikin gaggawa, sannan har an tura jam’ian tsaro sun rufe ofishin domin gudun ya shiga ya taba wasu takardun aiki.

Kawo yanzu a na rade-radin cewa za a maka tsohon Hadimin shugaban kasar gaban hukumar ICPC domin a gabatar da shi a kotu bisa laifin amfani da satifiket din bogi bayan dubun sa ta cika.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel