Wasu kungiyoyi na nan suna zanga-zangar neman a saki Sowore a Abuja

Wasu kungiyoyi na nan suna zanga-zangar neman a saki Sowore a Abuja

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an tsaurara matakan tsaro a babbar birnin tarayya Abuja, sakamakon fitowar da wasu kungiyoyi guda biyu suka yi, inda suke zanga-zangar neman a saki Omoyele Sowore, jagoran neman sauyi a gwamnatin Najeriya.

Daya daga cikin kungiyoyin mai suna The Guardians of Democracy and Development na zanga-zanga dangane daakan kisan 'yan sanda uku da farar hula daya da sojoji suka yi, bayan sun bude musu wuta a jihar Taraba 'yan makonni da suka wuce.

Ita kuma kungiyar Concerned Nigerians na neman a saki 'yan jarida da marubuta da hukumomin kasar suka tsare da suka hada madugun zanga-zangar juyin juya hali kuma tsohon dan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore.

An dai jibge jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda a dandalin Unity Fountain domin kwantar da tarzoma.

KU KARANTA KUMA: El-Zakzaky: Likitoci 186 daga kasashe 7 sun rubuta wa Buhari wasika (karanta)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hadakar kungiyoyin Arewa, CNG, ta zargi tsohon gwamnan Legas kuma babban jigo na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da munafunci bayan ya yi magana game da hadin-kai.

Wannan kungiya ta ce kalaman Bola Ahmed Tinubu su na cin karo da abubuwan da ya ke aikatawa.

A wani jawabi da kungiyar ta fitar a Ranar 12 ga Watan Agusta, 2019, ta yi kaca-kaca da ‘dan siyasar. Kakakin wannan kungiya ta CNG, Malam Abdulazeez Suleiman ya zargi Tinubu da hannu wajen hana a nada Inyamuri a matsayin Sakataren gwamnatin tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel