'Yan sanda sun kama kwararren mai kerewa 'yan fashi bindigu a Abuja

'Yan sanda sun kama kwararren mai kerewa 'yan fashi bindigu a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Najeriya a Abuja ta ce ta kama wani mutum da ke ya kware wajen kerewa kungiyoyin 'yan fashi da makami bindigu a babban birnin tarayyar.

Wanda ake zargin mai suna Michael Olajire yana daya daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban da kwamishinan 'Yan sandan Abuja, Bala Ciroma ya gabatar da su ga manema labarai.

Ya ce an kama su ne sakamakon binciken da sashin Yaki da Masu Fashi da Makami (SARS) na rundunar su ka yi yayin bincike kan wasu kungiyoyin 'yan fashi da su kayi suna wurin yi wa wadanda suka yi wa fashi fyade.

Kwamishinan 'Yan sandan ya ce an: kama wanda ake zargin ne a mabuyarsa da ke Byazine, Kubwa bayan kama wasu daga cikin 'yan kungiyarsa a shekarar 2018.

DUBA WANNAN: Tsohon kwamishinan 'Yan sanda ya fadi wadanda ke daukan nauyin 'yan bindiga a Najeriya

Ya kara da cewa, "An samu bindigan pistul da aka kera a gida Najeriya tare da alburusai biyu tare da shi. Za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan an kammala bincike."

Kazalika, Shugaban 'Yan sandan ya kuma ce rundunar ta kama wasu da ake zargi da yiwa mutane fashi a cikin motocin haya da aka fi sani da 'One-chance' da suka dade suna adabar mutanen Abuja da kewaye.

Ya ce, "A ranar 1 ga watan Yulin 2019, dakarun 'yan sanda na SARS sun bankado wata kungiyar 'yan one-chance da suke yi wa mutane fashi a tsakanin AYA (Asokoro), Kubwa, Zuba da Nyanya."

An kama su da wata mota kirar Golf dauke da ruwan sha na leda da aka fi sani da pure water domin batar da kama.

Wadanda aka kama sune: Oryu Ugo, Terdoo Zugo da Monday Godwin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel