Yanzu-yanzu: An gurfanar da surukin Atiku, Abdullahi Babalele a gaban kotu

Yanzu-yanzu: An gurfanar da surukin Atiku, Abdullahi Babalele a gaban kotu

Hukumar Yaki da Masu Yiwa Arzikin Kasa Zagon Kasa, EFCC ta gurfanar da Babalele Abullahi, surukin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar a gaban kotu.

An gurfanar da Babalele ne a safiyar ranar Laraba gaban mai shari'a Nicholas Oweibo na Babban Kotun Tarayya da ke Legas bisa tuhumarsa kan aikata laifuka biyu masu alaka da satar kudade.

Sai dai bai amsa laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

DUBA WANNAN: EFFC ta fara bincikar gwamnatin Obasanjo kan bannatar da $16bn don samar da lantarki

Justice Oweibo ya bayar da umurnin EFCC ta cigaba da rike Babalele a hannun ta har zuwa gobe Alhamis da za a saurari bukatar bayar da shi beli da lauyansa Mike Ozekhome (SAN) ya nema kotun ta bayar.

A cewar lauyan EFCC da ya gabatar da karar a gaban kotu, Rotimi Oyedepo, Babalele ya aikata laifin ne a watan Fabrairun 2019.

Takardar tuhumar ta ce Babalele ya taimakawa wani Bashir Mohammed biyan tsabar kudi $140,000.00 cikin wata asusun ajiya ba tare da bi da hukumomin da doka ta tanadar ba.

Tuhumar ta ce kudin ya wuce adadin da doka ta bayar da damar yin hada-hadar da shi a lokaci guda.

Hukumar EFCC ta ce laifin ya sabawa sashi na 18(c) na dokar hana karkatar da kudade ta shekarar 2011 da aka yi wa kwaskwarima kuma sashi na 16(2)(b) na dokar ya tanadar da hukuncin da ya dace da wanda ya aikata laifin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel