Jami'an tsaro sun hana likitoci su duba mu a asibitin kasar Indiya - Zakzaky

Jami'an tsaro sun hana likitoci su duba mu a asibitin kasar Indiya - Zakzaky

Shugaban kungiyar yan Shia, Ibrahim Zakzaky ya koka kan halin tsatstsauran matakan tsaro da aka sanya musu a asibitin daya tafi neman lafiya tare da matarsa a kasar Indiya, don haka ya nemi ya koma Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito Zakzaky ya bayyana haka ne cikin wani hira da yayi kuma aka nada, wanda a yanzu haka yana yawo a kafafen sadarwar zamani, inda yace jami’an tsaron Najeriya da na kasar Indiya sun hana likitocin asibitin Medanta na kasar Indiya su dubasu.

KU KARANTA: Ko nawa ne: Kungiyar yan Shi’an kasar Indiya sun yi alkawarin biyan kudin asibitin Zakzaky

Saurari cikakken jawabinsa Zakzaky a nan:

“Mun zo birnin Delhi a indiya domin neman lafiya na wasu matsaloli da muke tare da su, ni da Malama Zeenah. Ita Malama Zeenah akwai cikakken harsashi a jikinta, sannan kuma bayan haka nan akwai bukatar canjin kokon gwiwowinta guda biyu da kuma wasu matsaloli.

“Ni kuma akwai baraguzan harsasai wanda suka farfashe. 'Yan kanana a idanuna, da kuma wasu a hannuna, da kuma wasu a cinyata ta dama wanda sune suka rinka yin aman guba, wanda ya sabbaba matsaloli wanda daga baya muka gano sune suka sabbaba mini wannan "stroke" na farko da na biyu.

“Sannan kuma ina da matsalar ido, wanda shi ma har wala yau tuntuni likitocin da suka duba mu tun bayan da aka yi man operation na biyu ganina yai rauni, suka bada shawarar shi ma a je inda ya kamata domin ai aiki” Inji shi.

Daga karshe Zakzaky ya nemi a mayar dashi Najeriya don yin nazari kan halin da ake ciki, tare da duba yiwuwar zabi cikin wasu kasashe guda uku da suka nuna sha’awar amsansu, da suka hada da Maleshiya, Indoneshiya da kuma Turkiyya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel