Dan sanda ya harbe kansa a Amurka

Dan sanda ya harbe kansa a Amurka

Wani zakakurin jami'in dan sandan birnin New York na kasar Amurka, Robert Echeverria, ya harbe kansa murus har lahira.

Jami'in dan sandan mai shekaru 56 a duniya, ya harbe kansa da harashin bindigarsa ta aiki a cikin wani gidansa dake unguwar Laurelton da misalin karfe 6.00 na Yammacin ranar Talata kamar yadda hukumar 'yan sandan kasar ta bayyana.

Robert wanda ya yi bauta ta tsawon shekaru fiye da ashirin a karkashin hukumar 'yan sandan birnin New York ta kasar Amurka, ya debewa kansa tsammani a ranar Talata.

Bayan wannan muguwar aika-aika ta Robert ya yiwa kansa, a halin yanzu jami'an 'yan sandan kasar Amurka 9 ne suka kashe kansu cikin shekarar da muke ciki.

A yayin da babu wanda ya ke da masaniyar dalilin da ya sanya Robert ya debewa kansa tsammani, ana zargin mutuwarsa na da alaka da tabin hankali.

KARANTA KUMA: An nemi Buhari ya shiga tsakanin rikicin jihar Taraba

Wani makocin marigayi Robert mai shekaru 23 a duniya, Brendan Betts, shi ne ya yi wannan zargi tare da cewar mutuwar makocinsa ta yi matukar sosa masa zuciya.

Hukumar 'yan sandan birnin New York, NYPD, cikin wani sako da wassafa a shafinta na zauren sada zumunta, ta bayyana bakin cikin rashin daya daga cikin jami'anta da ya katsewa kansa hanzari ta hanyar kisan kai.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel