An nemi Buhari ya shiga tsakanin rikicin jihar Taraba

An nemi Buhari ya shiga tsakanin rikicin jihar Taraba

  • Wata kungiya ta nemi Buhari da ya shiga tsakanin rikicin da ya mamaye jihar Taraba
  • Kungiyar ta yi zangar-zanga a kan neman gano bakin zaren da ya haddasa rikici tsakanin kabilun Tibi da Jukun tsawon shekaru da su gabata
  • Masu zanga-zangar sun nemi gwamnatin Tarayya da ta dauki mataki kan masu haddasa fitina a jihar Taraba

Babu shakka a halin yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza samun sukuni yayin da aka huro masa wuta a kan tabbatar da kawo karshen rikicin da ke tsakanin kabilun Jikun da kuma Tibi a jihar Taraba.

A wata zanga-zanga da aka gudanar cikin Abuja a ranar Laraba, 14 ga watan Agusta, wasu 'yan asalin jihar Taraba da kuma wadanda lamari ke ciwa tuwo a kwarya, sun nemi shugaban kasa Buhari da shiga tsakanin rikicin da ya janyo asarar rayukan mutane da dama tsawon shekaru aru-aru.

Cikin wata rubutacciyar wasika zuwa ga shugaba Buhari da sa hannun madugun masu zanga-zangar, Mike Msuaan da kuma Solomon Adodo, sun roki gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta dauki mataki a kan masu haifar da fitina da rashin zaman lafiyar al'umma a jihar Taraba.

Masu zanga-zangar sun bayar da shaidar cewa, a halin yanzu su kansu kabilun Tibi da Jukun sun kosa wajen ganin sulhu ya tabbata a tsakaninsu wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

KARANTA KUMA: 'Yar kunar bakin wake ta kashe mutum 6 a Chadi

Sun kuma nemi shugaban kasa Buhari da ya umarci dukkanin hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki wajen bankado masu hura wutar rikicin da ke tsakanin kabilun biyu wanda ya ki ci ya ki cinyewa tsawon shekaru aru-aru.

A yayin haka gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku, ya bayar da tabbacin cewa ya na iyaka bakin kokarin sa tare da takwaransa na jihar Binuwai, Samuel Ortom, wajen kwantar da tarzomar da ta mamaye kabilun biyu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel