'Yar kunar bakin wake ta kashe mutum 6 a Chadi

'Yar kunar bakin wake ta kashe mutum 6 a Chadi

A ranar Larabar da ta gabata ne wata 'yar kunar bakin wake ta kai hari Yammacin kasar Chadi, inda ta salwantar da rayukan mutane shida yayin da ta tayar da bam din da ke jikinta kamar yadda wani jami'in tsaro ya bayar da shaida.

Ana zargin wannan mummunan hari na kungiyar masu tayar da kayar da baya ta Boko Haram ne kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

Mutane shida ne suka rasa rayukansu da suka hadar har da wani dakarun soja guda daya yayin mummunan hari da ya auku a gundumar Kaiga-Kindjiria inji wani babban jami'in sojin kasa da ya nemi a sakaya sunansa.

Ba tare da bayyana adadin su ba, kazalika harin na kunar bakin wake ya raunata mutane da dama da sanyin safiyar ranar Laraba, 14 ga watan Agustan 2019.

Wani jami'in tsaro a gundumar Kaiga-Kindjiria ya ce, macen 'yan kunar bakin wake ta shi da bam din da ta dauro shi a jikinta daura da fadar wata masarautar gargajiya.

Dogarai hudu da kuma wani jami'in soja guda daya, na cikin mutane shidan da suka riga mu gidan gaskiya yayin da kimanin mutane biyar suka jikkata.

KARANTA KUMA: Sojoji cikin maye sun kashe mutane 3, sun raunata 5 a Legas

Kakakin rundunar sojin kasa na kasar Chadi, Kanal Azem Bermandoa, ya bayar da tabbacin aukuwar wannan mugun ji da mugun gani.

Gundumar Kaiga-Kindjiria wani babban yanki ne a gabar tafkin Chadi da ke iyaka da kasar Kamaru, Chadi, Nijar da kuma Najeriya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel