Sojoji cikin maye sun kashe mutane 3, sun raunata 5 a Legas

Sojoji cikin maye sun kashe mutane 3, sun raunata 5 a Legas

Bayan sun yi mankas sanadiyar kwankwadar barasa da ta yi masu mugun karo, wasu sojoji sun harbe mutane uku murus har Lahira tare da raunata mutane biyar a daren ranar Litinin a wani yanki dake kan iyakar Legas da kuma Ogun.

Wannan mummunan lamari na zuwa ne bayan kimanin mako guda da wasu sojoji suka harbe jami'an 'yan sanda da ke bakin aiki a yankin Ibi na jihar Taraba, inda suka kashe mutane shida da suka hadar da fararen hula uku.

Sojojin wadanda ake zargin sun sabawa ka'idar aikinsu, sun bude wuta a kan dandazon mutane da ke gudanar da shagulgula na wani bikin al'ada ta ranar Isheri a yankin Kara bayan da aka nemi su daina shiga hanci da kudundune.

Yayin tuntubar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari mai cike da bakin ciki da cewar aikin gama ya gama domin kuwa babu ikon mayar da hannun agogo baya.

KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Buhari ya sha alwashin ganin bayan ta'addancin masu garkuwa da 'yan daban daji

A can kasar Chadi kuma, wata 'yan kunar bakin wake da ake zargin alakar ta da kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, ta kashe mutane shida da suka hadar har da wani dakarun soja guda a gundumar Kaiga-Kindjiria.

Mahukunta sun tabbatar da aukuwar lamarin cikin yankin Kaiga-Kindjiria dake gabar tafkin Chadi daura da iyakokin kasashen Kamaru, Nijar da kuma Najeriya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel