Rashin Tsaro: Buhari ya sha alwashin ganin bayan ta'addancin masu garkuwa da 'yan daban daji

Rashin Tsaro: Buhari ya sha alwashin ganin bayan ta'addancin masu garkuwa da 'yan daban daji

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin ganin bayan duk wasu kalubale na rashin tsaro da suka addabi kasar nan

- Shugaba Buhari ya ce masu tayar da tarzoma a kasar tare da kiran sunan Allah a yayin tafka ta'ada ba su da masaniya a kan sunan wanda suka kira

- Shugaban kasar ya ce gwamnatin tarayya za ta ribaci dakarun soji, 'yan sanda da dukkanin masu ruwa da tsaki wajen kawo karshen ta'addanci a Najeriya

A ranar Laraba 13 ga watan Agustan 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake sabunta alkawali inda ya sha alwashin cewa nan da shekaru hudu masu zuwa sai ya ga bayan duk wasu kalubale na rashin tsaro da suka yiwa Najeriya dabaibayi.

Da ya ke gabatar da jawabansa a birnin Katsinan Dikko, shugaba Buhari ya ce masu hannu cikin ta'adar garkuwa da mutane da 'ya daban daji basu da alaka ta kusa ko ta nesa da imani na musulunci.

Shugaban kasar ya ce masu zartar da wannan mummunar ta'ada ba su da masaniyar a kan Allah Madaukakin Sarki ko kuma ba su yi imani da shi ba.

Cikin kalamansa kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, shugaba Buhari ya ce, "Ina da tabbacin cewa a kullum muna bacci kuma mu farka da bacin rai akan ta'adar 'yan daban daji da kuma masu garkuwa da mutane a jihohi da kuma kasa daya.

Cikin ikon Rabbani za mu ribaci dakarun soji, 'yan sanda da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki domin ganin bayan duk wasu 'yan ta'adda a kasar nan."

Dukkanin masu zartar da ta'addanci ta hanyar zubar jini da kashe al'umma tare da kiran sunan Allah yayin aiwatar da hakan, kasurguman makaryata ne kurum domin kuwa Allah ya tsarkaka daga duk wani nau'i na zalunci."

Ba zai yiwu mutum ya ce 'Allahu Akbar' ba kuma ya ribaci bam ko bindiga ba, ko kuma adda ko wuka wajen kashe al'umma wadanda basu ji ba kuma basu gani ba. Wannan alama ce dake nuna cewa basu yarda da Allah ba kuma basu san abinda suke fada ba."

KARANTA KUMA: Ana zanga-zangar neman sakin El-zakzaky a Indiya

A ranar Laraba ne shugaba Buhari ya kai ziyara karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina inda ya jajanta tare da nuna alhini ga 'yan gudun hijira wanda tarnaki na ta'addanci ya raba su da muhallansu.

Karamar hukumar Batsari na daya daga cikin kananan hukumomi takwas da ta'addancin 'yan daban daji da kuma na masu garkuwa da mutane ya fi ta'azzara a jihar Katsina.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel