Kaico: 'Yan bindiga sun bi shugaban mafarauta da dansa har gida sun kashe su

Kaico: 'Yan bindiga sun bi shugaban mafarauta da dansa har gida sun kashe su

Wasu 'yan bindiga sun kashe dan shugaban mafarauta na Bunu, Caleb Oshe da dansa mai suna Sunday a garin Suku da ke karamar hukumar Kabba-Bunu na jihar Kogi.

Daily Trust ta ruwaito cewa wasu mutane dauke da bindigu sun kai hari gidan shugaban mafarautan wadda shine kuma shugaban 'yan kungiyar tsaro na sa kai a garin misalin karfe 3 na daren jiya Talata.

Daga bisani an gano cewa 'yan bindigan sun nemi a basu kudi sannan suka sace wasu kayayaki masu daraja.

A bangarensa, Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi Allah-wadai da kisar kuma ya bayar da umurnin gudanar da cikaken bincike domin gano wadanda suka aikata wannan mummunan lamari.

DUBA WANNAN: Zan karbo nasara ta a kotu - Dan takarar gwamnan PDP na jihar Niger

A jawabin da ya fitar da bakin Direkta-Janar dinsa na Watsa Labarai, Kingsley Fanwo, Gwamna Bello ya ce, "Gwamnati na da Jihar Kogi ba za ta amince da wannan ba"; yayin da ya yi kira ga al'umma su kame kansu domin an tura jami'an tsaro suyi bincike kan lamarin.

"A halin yanzu ba a san wanda ya aikata wannan kisar ba saboda haka kada wanda ya dauki doka a hannunsa. Baya ga kasancewa Shugaban Kungiyar Sa-Kai a Suku, marigayi Caleb shine shugaban masu harkar sare itace a garin.

"Duba da irin muhimmancin da garin Suku ke da shi ga siyasa da tattalin arzikin yankin, bamu da wata zabi illa mu bar jami'an tsaro su gudanar da cikaken binciken yadda aka aikata laifin. Zamu basu dukkan goyon bayan da suke bukata domin samun nasara."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel