Ba a kai hari tashar mota ba – Gwamnatin Kogi

Ba a kai hari tashar mota ba – Gwamnatin Kogi

-Gwamnatin Kogi ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa an kai harin bindiga a tashar Big Joe dake Lokoja

-Mai magana da yawun gwamnatin jihar Kogi Kingsley Fanwo ne ya bada wannan sanarwar ranar Talata

-'Yan jarida sun ziyarci wannan wurin inda suka tabbatar da cewa zancen karyane ake yadawa

Gwamnatin Jihar Kogi tayi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa ‘yan bindiga sun kai hari tashar motocin Big Joe dake Lokoja a ranar Talata.

A wani zancen da ya fito daga hannun kakakin gwamnan Jihar Kogi, Kingsley Fanwo ya bayyana labarin a matsayin karya gaba dayansa. Inda yake cewa, “ Wannan labarin wadansu ne masu son hada fitina ke watsa shi.”

KU KARANTA:Abinda ya hana Yahaya Bello halartar ganawar gwamnonin APC da Buhari – Garba Shehu

Akwai labarai da kuma hotuna da ke yawo a shafukan sada zumunta wadanda ke nuna cewa an kai hari tashar motan.

“ Labari ya same mu cewa ga abinda ke yawo a shafukan sada zumunta dauke da rahoto da kuma hotunan kai hari wata tashar mota dake Lokoja.

“ Muna so mu sanar da dukkanin matafiya masu shigowa ko fita daga Kogi cewa wani abu makamancin wannan bai faru ba, karya ce kawai wasu ke yadawa. Jami’an tsaron jiharmu na nan bisa kafafunsu suna aiki tabbatar da tsaro a jihar.” Inji Kakakin.

Har ila yau, kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN da ya ziyarci tashar motar ta Big Joe ya tarar da harkoki na gudana cikin tsanaki babu wata alamar rikici.

Wata mata mai sayar da abinci a tashar inda ta bayyana sunanta a matsayin Esther Nathaniel, ta ce a wurin wakilin NAN ta fara jin wannan labarin.

“ Ba gaskiya bane, a nan nake sayar da abinci da kuma lemu babu wani abu makamancin wannan ma da ya taba faruwa a nan.” Inji matar.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel