Sarkin Kano Sanusi II ya sake samun wani mukami daga kasar waje

Sarkin Kano Sanusi II ya sake samun wani mukami daga kasar waje

Wata kungiyar kasar Kanada mai suna “1Million Teachers Inc”, ta nada Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a matsayin Shugaban kwamitin ba ta shawara a Najeriya.

Basaraken ya kuma kasance mamba a kwamitin iyaye na kungiyar, 1 Million Teachers Canada.

A cewa wata sanarwa a ranar Talata, 13 ga watan Agusta kungiyar ta 1Million Techers Inc. “ta bayar da damar samun ingantaccen ilimi ga malamai a fadin duniya.

Jawabin ya kawo inda shugban kungiyar, Hakeem Subair ya nuna jin dadinsa akan nadi Sanusi.

“Hakan wani Karin karfi ne ga tawagar. A koda yauhe kungiyar 1Million Teahers na neman muryoyi masu fada a ji, domin taimaka mana wajen cimmamanufarmu na inganta harkar ilimi ga kowa, musamman iyaye mata da yara mata.

KU KARANTA KUMA: An yi wa Sanatoci da 'Yan Majalisa gwajon manyan motoci a araha banza

“Don haka, muna yiwa mai martaba, Muhammad Sanusi II, sarkin Kano maraba da zuwa, a matsayin Shugaban, kwamitin ba da shawara na 1 Million Teachers."

A wani labari kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta ce maganar binciken Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II kan zarginsa da almundahanar wasu kudade mallakar masarautar na nan daram duk da cewa ya yi sulhu da Ganduje.

Hukumar ta ce: “Muna aiki ne a matsayinmu na hukuma mai zaman kanta bisa la’akari da abinda ya bayyana gabanmu daga wasu dake da kusanci da masarautar tun ranar 28 ga watan Maris, 2017.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel