Likitoci sun fara duba Zakzaky, sun gano cututtuka 8

Likitoci sun fara duba Zakzaky, sun gano cututtuka 8

Shugaban kungiyar IMN wanda akafi sani da Shi'a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat sun fara samun kula daga likitocin asibitin Medanta dake kasar Indiya.

Zakzaky da matarsa sun dira kasar Indiya ranar Talata tare da yan'uwa, jami'an tsaro da ma'aikatan gwamnati.

Likitoci sun ce El-Zakzaky na fama da cututtuka takwas wanda kunshi glaucoma, ciwon zuciya, rashin iya bacci.

Kana akwai harsasai a cikin jikinsa tun shekarar 2015 da soji suka harbesa a Zariya. Wadannan harsasai na haifa masa wasu cututtuka cikin jininsa.

Likitoci sun fara duba Zakzaky, sun gano cututtuka 8

Zakzaky
Source: UGC

El-Zakzaky wanda ya kasance a tsare hannun hukumar DSS tun 2015 yana gurfana a kotu kan laifuffuka da dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel