Tsohon kwamishinan 'Yan sanda ya fadi wadanda ke daukan nauyin 'yan bindiga a Najeriya

Tsohon kwamishinan 'Yan sanda ya fadi wadanda ke daukan nauyin 'yan bindiga a Najeriya

Tsohon kwamishinan 'Yan sandan jihar Legas, Abubakar Tsav ya ce 'yan siyasa ne ke daukan nauyin 'yan bindiga da ke adabar al'umma a sassa daban-daban na Najeriya.

A jawabin da ya yi a ranar Talata 13 ga watan Augustan 2019 a Makurdi, Tsav ya ce 'yan siyasa ne ke daukan nauyin mafi yawancin hare-haren da ake kai wa a kasar. Ya ce mafi yawancin 'yan siyasan sun san 'yan bindigan sun kuma san dalilin da yasa suke aikata hakan.

Tsav ya ce, "Yan siyasa ne ke daukan nauyin 'yan bindiga kuma sun san 'yan bindigan. Sun san dalilan da yasa 'yan bindigan suke kai hare-haren. Ina kira ga 'yan siyasan mu su canja tunanin su su bawa jami'an tsaro hadin kai domin a rage laifuka a bayan kasa.

DUBA WANNAN: Zan karbo nasara ta a kotu - Dan takarar gwamnan PDP na jihar Niger

"Idan 'yan sanda za su iya jarumta su bincika gidan 'yan siyasa kuma su ringa sanya ido kan abubuwan da su keyi, za suyi mamakin irin abubuwan da za su gano."

Ya kuma ce karuwar rashawa da rashin tsaro a iyakokin kasar yana taimakawa wurin tsananta kallubalen tsaro a kasar duba da cewa ta iyakokin kasar ne ake shigo da haramtattun makamai.

Tsav ya shawarci gwamnatin tarayya da dauki sabbin ma'aikata a hukumomin tsaro domin hakan zai rage yawan matasan da ke yawo a tituna marasa aikin yi da rage laifuka a kasar.

A cewarsa, hukumomin tsaro musamman 'yan sanda suna da karancin ma'aikata da za su iya kulawa da matsalolin rashin tsaro da ake fama da su a kasar duba da cewa mafi yawancin su suna gadin 'yan siyasa ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel