Gwamnan jihar Borno ya bayar da dajin Sambisa domin kafa Ruga

Gwamnan jihar Borno ya bayar da dajin Sambisa domin kafa Ruga

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara, ya bayar da wasu bangarori na yankin Boko Haram, dajin Sambisa, domin kafa shirin Ruga.

Gwamnan ya kuma zuba jami’an NSDC, da maharba domin su tsare ilahirin dajin da kuma tabbatar da tsaron shirin.

Dajin da aka bayar ya shafe yankuna shida na Konduga, Bama, Gwoza, Chibok, Damboa da kuma Askira/Uba.

Gwamnan ya yanke shekarar ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi bakuncin Shehun Borno, Alhaji Garbai El-Kanemi, wanda ya kai masa ziyarar Sallah.

Yace an zuba jami’an tsaron ne domin su kare makiyaya da manoma a garuruwansu daban-daban.

Umara ya fada ma sakin cewa gwamnatin jihar a ta kuma zuba twagar bayar da agajin gaggawa, da suka hada da jami’an tsaro, domin ba al’umma kariya daga yan ta’addan Boko Haram da kuma yan bindiga.

KU KARANTA KUMA: An yi wa Sanatoci da 'Yan Majalisa gwajon manyan motoci a araha banza

A cewar gwamnan, “Wannan gwamnati ta jajirce don karfafa lamarin tsaro da kuma karfafa ayyukan makiya a manoma a fadin jihar."

Umara yace tawagar tsaro sun hada da dakarun sojoji da maharba 500 wadanda suka san ciki da wajen dajin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel