Obaseki ‘Danuwa na ne, babu rigimar da mu ke yi Inji Oshiomhole

Obaseki ‘Danuwa na ne, babu rigimar da mu ke yi Inji Oshiomhole

Mun samu labari cewa shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Adams Oshiomhole, ya zargi ‘yan jarida da laifin kirkirar rigima tsakaninsa da gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo.

Adams Oshiomhole ya bayyana cewa wasu tsirarrun mutane ne da ke da wata manufar siyasa su ka haddasa rigima tsakaninsa da gwamnan na sa. Oshiomhole ya ce gwamnan ‘danuwa ne a wurinsa.

Shugaban jam’iyyar na APC ya yi wannan magana ne bayan wani dogon zama da ya yi da gwamna Godwin Obaseki a gidansa da ke cikin Iyamoh a cikin karamar hukumar Estako ya Yamma jiya.

Oshiomhole ya yi magana da Manema labarai bayan zaman da ya yi gwamnan a bayan labule a Ranar Talata. Oshiomhole ya nuna cewa zaman na su ba bakon abin ba ne domin su kan gana bini-bini.

“Wannan ziyara ba bakuwar abu ba ce, zaman da a ka yi ya ba ni damar ganawa da ‘Danuwa na (Obaseki) da kuma mutanen da na yi aiki da su.” Inji tsohon gwamnan na Edo kuma shugaban APC na kasa.

KU KARANTA: Shugaban APC, Buhari da Tinubu sun kauracewa bikin Oyegun a Edo

A na sa bangaren, Mai girma gwamna Godwin Obaseki shi ma ya bayyana cewa babu abin surutu game da wannan taron. Ya ce: “Mun zo ne mu yi bikin murnar babbar sallah tare da tsohon Maigidana."

Gwamnan ya kara da cewa masu tunanin akwai rikici tsakaninsa da Oshiomhole, su daina wannan tunani. Rigimar Adams Oshiomhole da Magajinsa ta fito fili ne wajen kafa majalisar dokoki a bana.

Sai dai duk da jita-jitar rashin jituwar, gwamnan ya birne wannan rade-radin inda ya kai wa Maigidan na sa ziyara har gida cikin dare a lokacin da Musulman Duniya su ke bikin babbar idin sallah.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel