An yi wa Sanatoci da 'Yan Majalisa gwajon manyan motoci a araha banza

An yi wa Sanatoci da 'Yan Majalisa gwajon manyan motoci a araha banza

Bayanai sun billo kan yadda aka siyar da kayayyakin majalisar dokokin kasa a lokacin ficewar majalisa ta takwas kafin rantsar da majalisa ta tara da aka yi kwanakin baya.

An kuma yi zargin cewa akwai badakala a kwangilar sake fentin ofishohin mambobin majalisar dokoki ta tara, yayinda aka rasa cikakken bayani kan yadda aka tafiyar da tsarin.

Binciken New Telegraph akan yadda aka siyar da yawancin kayayyakin majalisar dokokin da yan majalisa ta takwas suka yi amfani da shi ya nuna cewa hukumomin majalisar sun hada kai da mambobin majalisar wajen siyar da kayayyakin akan karyayyen farashi.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka siyar wa mambobin majalisar dattawa da na majalisar wakilai akan farashi mai ban mamaki sun hada da mota kirar Toyota Land Cruiser, na’urar kwamfuta, na’urar fotokofi, firinji da dai sauransu.

An tattaro cewa hukumar majalisar tarayyar sun bayar da motoci kirar Toyota Land Cruiser, Sport Utility Vehicle (SUV), wanda aka siya tsakanin naira miliyan 24 da naira miliyan 26 kowanne, ga sanatoci da yan majalisar wakilai akan naira miliyan 1 kacal.

An kuma tattaro cewa hukumar majalisar tarayyar ta karbi naira 360,000 kacal a hannun yan majalisar a matsayin kudaden setin talbijin guda biyu, na’urar fotokofi, na’uarar kwamfuta da kuma wani babban firinji.

Hakan ya faru ne a karshen zangon majalisar da ta gabata lokacin da hukumar ke daukar bayanai kan aubuwan da suka tanadarwa yan majalisar domin amfaninsu a tsakanin 9 ga watan Yuni 2015 zuwa 11 ga watan Yuni 2019, domin a tanadarwa mambobin majalisa mai ci kayayyakin aiki.

An rahoto cewa za a sake siyan dukkanin kayayyakin wanda kusan a kyauta a baiwa yan majalisa da suka gabata, sannan a gabatar da su ga mambobin majalisar tarayya ta tara, wanda aka rantsar a ranar 11 ga watan Yuni 2019.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Najeriya za ta tarwatse kuma 'yan arewa ne za su ji jiki - Sheikh Gumi

Wata majiya ta majalisar dokoki, wacce ta nemi a boye sunanta, ta bayyana cewa motar Toyota SUV, wanda aka yi gwanjon su akan naira miliyan daya kacal, an siye su ne akan naira miliyan 24 da 26 kowani guda a lokacin da aka gabatar da su ga yan majalisar a 2015.

Majiyar ta kuma bayyana cewa a wancan lokacin an siyi kowani talbijin kan naira miliyan 2.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel