Taraba: ‘Dan Sandan ya tsallake rijiya da baya ya fadi abin da ya faru

Taraba: ‘Dan Sandan ya tsallake rijiya da baya ya fadi abin da ya faru

A na cigaba da bankado abubuwan da su ka faru a makon da ya gabata a lokacin da wasu jami’an sojojin Najeriya su ka kai wa Dakarun ‘yan sanda na IRT hari ba tare da sun sani ba a jihar Taraba.

Wani Jami’in ‘Dan sanda da ya tsira da kyar ya bayyana cewa saura kiris ya bakunci lahira bayan da wani Soja ya nemi a harbe shi a kai. Yanzu haka dai ya na jinyar harbin da sojojin kasar su ka yi masa.

“Allah ne dai ya yi ina da sauran kwana. Mun damke wani Mai satar mutane mun sa a cikin motar mu kenan, mun wuce bakin iyakokin Sojoji biyu, a lokacin da mu ka yi gaba sai mu ka ga a na bin mu.”

“A hankali mu ke tafiya, mu na jiran wannan motar sojoj ta wuce mu. Kwatsam sai a ka bude mana wuta. A nan motar mu ta yi kundunbula, ni kuma harsashi ya same ni a kafa, inda na sheka cikin daji.”

KU KARANTA: Kwamacala bayan Sojoji sun 'kashe' 'yan sanda 3 a Taraba

“Daga nesa na hangi yadda Sojoji su ka aika Abokan aiki na lahira. Bayan nan su ka shiga cikin dajin su na neman wadanda su ka tsere. A nan a ka cafko ni, har wani ya bada shawarar a harbe ni a kai.”

“Na taki sa’a wani jami’in ya ce a kai ni asibiti. Ba domin shi ba, da na mutu nima. Bayan nan ne mutanen Kauyen su ka fito su na daukar abin da ya faru, a dalilin haka Sojojin su ka fasa harbe ni.”

Jaridar Vanguard ta rahoro cewa wannan Jami’in na ‘yan sanda ya ce ya na kallo wadannan Dakarun Sojoji su ka dauke wannan mai laifi da su kama, su ka sa shi a cikin motarsu, su ka yi gaba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel