Abinda ya hana Yahaya Bello halartar ganawar gwamnonin APC da Buhari – Garba Shehu

Abinda ya hana Yahaya Bello halartar ganawar gwamnonin APC da Buhari – Garba Shehu

-Garba Shehu ya fadi dalilin da ya hana Gwamnan Kogi zuwa Daura wurin Shugaban kasa

-Gwamna Yahaya Bello yayi rashin kishiyar mahaifiyarsa ne wanda ya zama dalilin hana shi zuwa Daura wurin Shugaba Buhari

-Shugaban kasa da Shugaban majalisar dattawa sun mika sakon ta'aziyyarsu ga Gwamnan Jihar Kogi

Malam Garba Shehu yayi bayani a kan dalilin rashin halartar Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello garin Daura domin ganawa da Shugaba Buhari kamar yadda sauran takwarorinsa na APC suka yi.

Mataimakawa Shugaban kasa a kan lamuran yada labarai ya fitar da wannan jawabin ne ranar Talata jim kadan bayan gwamnonin APC sun ziyarci Shugaban kasa a garinsa na haihuwa wato Daura ta Jihar Katsina.

KU KARANTA:Idan kazo Daura kadai muke samun wuta, hakiman yankin Daura sun shaidawa Buhari

Ya ce, gwamnan bai samu zuwa bane saboda rasuwar kishiyar mahaifiyarsa, halartar jana’iza da sauran abubuwa ne suka shige masa gaba.

Shugaba Buhari yayi juyayin rasuwar Hajiya Rakiya Momoh Bello , inda ya mika sakon ta’aziyya ga gwamnan tare da fatan Allah ya jikanta da gafara.

“ Gwamnan Kogi bai samu kasancewa tare da Shugaban kasa ba da kuma takwarorinsa na APC a dalilin rasuwar kishiyar mahaifiyarsa Hajiya Rakiya. Shugaban kasa ya lura cewa ba ya nan amma a sanar da shi cewa anyi masa rasuwa ne don shi bai samu zuwa ba.” A cewar Shehu.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya wadda aka fi sani da NGF, Kayode Fayemi kuma gwamnan jihar Ekiti shi ya jagoranci tawagar gwamnonin zuwa Daura.

Bugu da kari, tare da Fayemi akwai gwamnonin jihohin Legas, Kebbi, Kaduna, Edo da kuma Katsina.

Shugaban majalisar dattawa Lawan Ahmad ya fitar da sakon ta’aziyyarsa ga gwamnan ta hannun kakakinsa Ola Awoniyi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel