Fasto Augustine Akubeze ya ce Buhari ba ya jin kukan mutanen Najeriya

Fasto Augustine Akubeze ya ce Buhari ba ya jin kukan mutanen Najeriya

Babban Limamin Darikar Katolika ta Mabiya addinin Kirista a Garin Benin da ke cikin jihar Edo, Augustine Akubeze, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai jin kukan mutane.

Faston ya yi wannan koke ne a wajen bikin da a ka shirya domin taya Cif John Oyegun murnar cika shekara 80. An yi wannan taro ne a cocin St. Paul Catholic Church da ke babban birnin Benin.

Augustine Akubueze ya ke cewa “Dole mu yi magana, mafi yawan jama’a ba su jin dadin halin rashin tsaro a kasar nan. Gwamnati ba za ta ce ta na da iko a kasa, idan ba za ta iya maganin ‘yan ta’adda ba.”

Faston ya cigaba da cewa: “Daga Yankin Arewa zuwa Kudu, daga Gabas zuwa Yamma, daga Tsakiyar Arewa zuwa Tsakiyar Yamma, mutanen Najeriya su na wani zama ne na dar-dar a kullum.”

“Da-dama na mutanen Najeriya su na jin cewa gwamnatin tarayya ba ta sauraronsu. Akasarin mutane su na ganin cewa sha’anin tsaro ne ya kamata a fi maida hankali a kai.” Inji wannan Limami.

KU KARANTA: Shugaban PDP da wasu 'Yan siyasa sun taya tsohon shugaban APC murnar cika shekaru 80

A jawabin da wannan Bawan Allah ya yi, ya ce: “Bai kamata a siyasantar da rashin rayuka da dukiyoyin mutane ba. A wasu kasashen, jama’a su na zama ne su hada-kai domin su yi maganin ta’addanci.

Wannan Malami na Darikar Katolika ya kuma bayyana cewa ya kamata ‘yan siyasa su damu ko da ran mutum daya a ka rasa, Malamin ya ce kuma bai kamata a rika nuna banbancin addini ko siyasa ba.

A karshe Akubeze ya jinjinawa John Oyegun a wannan rana inda ya kuma yi kira ga gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da shugaban APC mai-ci, Adams Oshiomhole su hada-kai, su daina rigima.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel