Oyegun @ 80: Secondus ya halarci biki, manyan APC sun ki zuwa

Oyegun @ 80: Secondus ya halarci biki, manyan APC sun ki zuwa

Manyan jagororin jam’iyyar APC na kasa ba su halarci bikin da a ka shirya domin taya Cif John Odigie-Oyegun murnar cika shekaru 80 a Duniya ba. John Oyegun shi ne tsohon shugaban APC.

An shirya biki ne a Ranar Litinin 12 ga Watan Agusta, 2019, domin taya Dattijon murnar zagayowar ranar haihuwarsa tare da murna ta musamman na shafe shekaru 80 da haihuwa.

Sai dai mun samu labari cewa manyan APC ba su halarci wannan biki da a ka yi a Garin Benin na jihar Edo ba. Abin mamaki, an hangi manyan jam’iyyar hamayya a wajen bikin da a ka shirya.

Uche Secondus, wanda shi ne shugaban PDP na kasa, da shugaban PDP na jihar Edo watau Cif Dan Orbih su na wajen taron inda su ka taya tsohon shugaban na APC zagayowar wannan rana.

KU KARANTA: Buhari ya gana da wasu manyan Jam'iyyar APC a Daura

Tsohon gwamna Lucky Igbinedion wanda yanzu ya na cikin manyan PDP a yankin ya na wajen wannan biki. Shi kuma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya turo wakilinsa ne a taron.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya ke bikin sallah a Daura ya aika ne da sakon taya murna. Haka zalika ba a ga keyar babban jigon jam’iyya, Bola Tinubu a wajen wannan taro ba.

Shugaban APC na kasa a yanzu kuma tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole, shi ma bai samu zuwa ba. Daga cikin gwamnonin APC kuwa, Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ne kurum ya je.

Gwamnan jihar Edo, da mataimakinsa da Sakataren gwamnati da kuma Kakakin majalisar dokoki duk su na wajen. Haka zalika an hangi Ministan da zai fito daga jihar Edo watau Osagie Ehanire.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel