Akwai munafunci a lamarinka – Kungiyar Arewa ta fadawa Tinubu

Akwai munafunci a lamarinka – Kungiyar Arewa ta fadawa Tinubu

Hadakar kungiyoyin Arewa, CNG, ta zargi tsohon gwamnan Legas kuma babban jigo na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da munafunci bayan ya yi magana game da hadin-kai.

Wannan kungiya ta ce kalaman Bola Ahmed Tinubu su na cin karo da abubuwan da ya ke aikatawa. A wani jawabi da kungiyar ta fitar a Ranar 12 ga Watan Agusta, 2019, ta yi kaca-kaca da ‘dan siyasar.

Kakakin wannan kungiya ta CNG, Malam Abdulazeez Suleiman ya zargi Tinubu da hannu wajen hana a nada Inyamuri a matsayin Sakataren gwamnatin tarayya. Suleiman a jawabin na sa ya ke cewa:

“Kalaman da Tinubu ya yi sun kara fito da munafuncinsa ne da yaudararsa a fili bayan yunkurin da ya rika yi na raba kan al’ummar Najeriya tare da jawowa wannan gwamnatin rashin yardar jama’a a da”

Ba mu hassada ga damar da Tinubu ya samu inda har ya ke ganin zai nemi takarar shugaban kasa ko ta karfi da yaji, amma akwai ban dariya ganin yadda ya dauka jama’a sun manta ko shi wanene”

Sulaiman ya zargi Jagoran APC da kawo sabani tsakanin al’umma inda ya jefa masa wasu tambayoyi:

KU KARANTA: Dole mu bi a hankali, mu yi hattara da Jega – Tsohon Shugaban PRP

“Tinubu ya fito ya yi wa jama’a bayanin i na ya kai batun hadin kai a lokacin da Sarkin Legas wanda su ke tare da shi, ya fito ya na kira a fatattaki duk wani Inyamurin da ba zai zabi jam'iyyar APC ba.”

Wannan kungiya ta kuma zargi da cewa Tinubu ya yi amfani da ‘Yan OPC wajen hana Inyamuran yin zabe a 2019. CNG ta kuma koka da yadda Tinubu ya hana Akinwumi Ambode dawowa kujerar gwamna.

“Ina maganar hadin-kan da Tinubu ya ke yi a lokacin da kungiyarsu ta Afenifere ta nemi Fulani su bar jihohin Kudu maso Yamma. Ina Tinubu ya shige lokacin da gwamnati ta ke batun gina RUGA?” Inji CNG

CNG ta kuma kara da cewa babban ‘dan siyasar ya yi gum a lokacin da Omoyele Sowore ya tado da maganar kawo juyin juya-hali a kan gwamnati mai-ci inda jama’a da dama a yankin su ka mara masa baya.

A karshe kungiyar ta nemi Tinubu ya wanke kansa kan yakinsa da Saraki da Amaechi don sun hana sa tsayawa takara a 2015, inda ta ce idan ba haka ba, kiran da ya ke yi na hada-kai, duk surutu ne.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel