Sanata Omo Agege ya bayyana musabbabin ziyarar da suka kai ma Buhari a Daura

Sanata Omo Agege ya bayyana musabbabin ziyarar da suka kai ma Buhari a Daura

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ovie Omo-Agege ya bayyana babban dalilin da yasa suka kai ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a gidansa dake garin Daura yayin bikin babbar Sallah.

A jawabinsa, Sanatan yace sun kai ma shugaba Buhari ziyarar ne domin bashi tabbacin samun goyon bayansu wajen aiwatar da dukkanin manufofinsu a sabuwar wa’adin gwamnatinsa na Next Level.

KU KARANTA: Ko nawa ne: Kungiyar yan Shi’an kasar Indiya sun yi alkawarin biyan kudin asibitin Zakzaky

A ranar Litinin, 12 ga watan Agusta ne Sanata Omo Agege tare da wasu gwamnonin jam’iyyar APC guda 10 suka kai ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyarar barka da Sallah, a karkashin jagorancin gwamnan jahar Kebbi, Atiku Bagudu.

Omo Agege yace: “Mun ga dacewar tunda dai shugaban majalisar dattawa yana can kasar Saudiyya yana yi ma Najeriya addu’a, don haka muka taho don wakiltarsa tare da majalisar gaba daya mu taya shugabanmu murnar barka da sallah.

“Kun san muna fama da irin matsalolinmu, amma duk da haka shugaban kasa yana kokarin tafiyar da akalar kasar yadda ya kamata, shi yasa muka ziyarceshi don taya shi murna, tare da bashi tabbacin goyon bayan majalisa, musamman majalisar dattawa wajen aiwatar da manufofin sabuwar gwamnatinsa.” In ji shi.

Sauran gwamnonin da suka ziyarci Buhari sun hada da Aminu Bello Masari, Nasir El-Rufai, Mohammad Badaru, Inuwa Yahaya na Gombe, Godwin Obaseki na Edo, Babajide Sanwo-Olu na Legas, Abdullahi Sule na Nassarawa, Kayode Fayemi na Ekiti da Gboyega Oyetola na Osun, sai kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel