Zan zamo garkuwa ga talakan Najeriya a sabon wa’adin mulkina – Buhari

Zan zamo garkuwa ga talakan Najeriya a sabon wa’adin mulkina – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai yi amfani da wa’adin mulkinsa na biyu wajen yi ma talakawan Najeriya yaki ta hanyar ianganta rayuwarsu, tare da zama garkuwa a garesu daga sharrin azzalumai.

Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata, 13 ga watan Agusta a garin Daura yayin da al’umman kananan hukumomin masarautar Daura guda biyar suka kai masa ziyarar Sallah a gidansa, inda yace ya gamsu cewa yan Najeriya sun fahimci aniyarsa, shi yasa suka sake zabensa a karo na biyu.

KU KARANTA: Tambuwal ya raba ‘Goron Sallah’ naira miliyan 70 ga alhazai 3,496

“Kun san irin wahalar da na sha kafin na kai ga wannan matsayi, sau uku ina tsayawa takara, sai a karo na hudu na samu nasara, Allah cikin hikimarsa Ya yi amfani da kimiyya da fasaha wajen samun nasarata, a karo na biyar dana sake tsayawa kuwa na zagaye kasar nan gaba daya, kuma jama’a sun yi maraba dani.

“Zamu mayar da hankali kan alkawurra uku da muka dauka da suka kunshi tsaro, tattalin arziki, da yaki da rashawa, za mu yi ma talakan Najeriya yaki. Zan nada ministan noma wanda ya san abin da yake yi, kuma ya san yadda hakan zai samar da ayyuka tare da habbaka tattalin arzikin kasa, zamu taimaka ma manomanmu.” Inji shi.

A nasa jawabin, shugaban tawagar, Yusuf Mai’aduwa, ya gode ma yan Najeriya da suka sake zaben shugaba Buhari, inda ya bada tabbacin ba zai baiwa yan Najeriya kunya ba, shima wani daga cikin jama’an, Mohammed Saleh, ya yaba ma Buhari bisa sanya hannu kan kudurin samar da kwalejin kimiyya da fasaha a garin Daura.

Daga karshe jama’an sun yi addu’ar Allah Ya taimaki shugaban kasa Buhari wajen jagorantar al’amuransa domin ya ciyar da Najeriya gaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel