Buhari ya umarci CBN ta daina bawa masu shigo da kayan abinci tallafi

Buhari ya umarci CBN ta daina bawa masu shigo da kayan abinci tallafi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ya umarci babban bankin kasa (CBN) da ya daina bayar da tallafin canjin kudi ga masu kasuwancin shigo da abinci cikin Najeriya.

A wani jawabi Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari, ya fitar, ya ce shugaban kasa ya bayar da wannan umarni ne domin inganta cinikin kayan abincin da aka noma a cikin gida.

Da yake karbar bakuncin manyan 'ya'yan jam'iyyar APC a gidansa na garin Daura, shugaba Buhari ya ce gwamnati zata yi amfani da kudin tallafa wa masu shigo da kayan abinci wajen inganta tattalin arziki.

"Kar ku kara bayar da tallafin ko Sisi ga duk wani shigo da kayan abinci cikin Najeriya," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Manajan banki ya kashe kansa, ya bar wa matarsa wata wasika mai ban mamaki

Shugaba Buhari ya bayyana cewa wasu jihohin Najeriya da suka hada da Kebbi, Ogun, Lagos, Jigawa, Ebonyi da Kano tuni suka yi amfani da damar da gwamnatin tarayya ta bullo da ita wajen inganta harkokin noma a jihohinsu.

"Mun samu cigaba a bangaren noman kayan abinci, muna yin kokari a wannan bangare," a cewarsa.

Buhari ya bayyana cewa ya yi matukar farin cikin ganin yadda 'yan Najeriya, da suka hada da matasa da suka kammala karatu, suka rungumi harkokin noman abinci a matsayin hanyar samun kudin shigo wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel