Fadar shugaban kasa ta yi gum a kan sallamar Ita Enang daga mukaminsa

Fadar shugaban kasa ta yi gum a kan sallamar Ita Enang daga mukaminsa

Rahotanni su na yawo cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi waje da Sanata Ita Enang daga mukamin da ya ke kai na bada shawara a kan harkokin majalisar dattawa a Najeriya.

Kawo yanzu dai fadar shugaban kasa ba ta fitar da wani cikakken bayani game da wannan labari ba. Sai da ma, Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya yi bakam a kan lamarin.

Malam Garba Shehu wanda ya ke magana a madadin shugaban kasa, ya nemi ‘yan jarida su tuntubi Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a lokacin da a ka yi masa tambaya a kan sallamar Hadimin.

Shehu ya ke cewa ‘yan jarida: “Sakataren gwamnatin tarayya ne zai yi magana a kan halin da a ke ciki.” A baya shugaban kasar ya maye gurbin Takwaran Ita Enang watau Kawu Sumaila bayan ya shiga takara.

KU KARANTA: Mai ba Shugaba Buhari shawara a Majalisa zai yi takara a APC

Sai dai Ita Enang bai amsa kiran da ‘yan jarida su ka yi masa domin jin ta bakinsa ba. Kamar yadda mu ka ji labari an yi yunkurin tuntubar Hadimin shugaban kasar a jiya 12 ga Agusta, amma ba a same shi ba.

A Ranar 11 ga Agusta mu ka samu wannan labari, Majiyar ta bayyana cewa shugaba Buhari ya sauke Ita Enang daga matsayin da ya ke kai tun 2015 na mai taimaka masa a kan sha’anin majalisar dattawa.

Ita Enang shi ne wanda ke shiga tsakanin Sanatocin kasar da kuma fadar shugaban kasa. Shi kan sa Enang ya aiki a majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar PDP inda daf da zaben 2015 ne ya koma APC.

A na jita-jitar cewa Sanata Omoworare Babajide, ne ya maye gurbin tsohon Sanatan na Akwa Ibom. Omoworare Babajide tsohon Sanata ne wanda ya wakilci jihar Osun a majalisar dattawan Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel