Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnoni da manyan yan APC a Daura (hotuna)

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnoni da manyan yan APC a Daura (hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnonin APC da sauran manyan masu ruwa da tsaki a Daura, jihar Katsina a ranar Talata, 13 ga watan Agusta.

Manyan jiga-jigan jam’iyyar mai mulki sun kai wa Shugaban kasar gaisuwar babban sallah ne a gidansa da ke mahaifarsa na Daura.

Gwamnonin a suka hallara sun hada da na jihar Katsina, Aminu Bello Masar; gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi; gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo Olu; gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da kuma gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnoni da manyan yan APC a Daura (hotuna)

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnoni da manyan yan APC a Daura
Source: Facebook

Sauran manyan masu ruwa da tsakin da suka hallara sun hada da Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari; Shugaban NITDA, Isa Ali Pantami da kuma mukaddashin Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, da dai sauransu.

KU KARANTA KUMA: Buhari shugaba ne kuma abun koyi ga yan Najeriya – Inji jigon jam’iyyar adawa

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnoni da manyan yan APC a Daura (hotuna)

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnoni da manyan yan APC a Daura
Source: Facebook

Ga karin hotunan da hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau ya wallafa a shafinsa na Facebook kasa:

A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi waje da Sanata Ita Enang daga mukamin da ya ke kai na bada shawara a kan harkokin majalisar dattawa a Najeriya.

Kawo yanzu dai fadar shugaban kasa ba ta fitar da wani cikakken bayani game da wannan labari ba. Sai da ma, Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya yi bakam a kan lamarin.

Malam Garba Shehu wanda ya ke magana a madadin shugaban kasa, ya nemi ‘yan jarida su tuntubi Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a lokacin da a ka yi masa tambaya a kan sallamar Hadimin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel