Wani babban jigon PDP ya yaba ma gwamnatin Buhari akan shirin Ruga

Wani babban jigon PDP ya yaba ma gwamnatin Buhari akan shirin Ruga

Sanata Walid Jibrin, Shugaban kungiyar amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bukaci yan Najeriya da su rungumi shirin Ruga na Gwamnatin Tarayya.

Jibrin ya bayyana ma manema labarai a gidansa da ke Nassarawa a ranar Talata, 13 ga watan Agusta cewa shirin zai inganta zaman lafiya da tsaro a kasar.

Har ila yau ya bayyana cewa shirin zai bunkasa tsaron kayan abinci da kuma inganta kiwon lafiya da rayukan al’umman karkara.

Jibrin, wanda ya kasance Sarkin Fulani a jihar Nassarawa ya ce ya jinjinawa Gwamnatin Tarayya akan shigo da shirin Ruga a kasar idan aka yi la’akari da muhimmancinta.

Jigon na PDP har ila yau ya yi kira ga kungiyoyin kabilun Igbo da Yarbawa da su rungumi shirin don tabbatar da cigaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Buhari shugaba ne kuma abun koyi ga yan Najeriya – Inji jigon jam’iyyar adawa

Haka zalika yayi kira ga dukkan makiyaya da sauran yan Najeriya da su guji fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran abubuwa marasa kyau don samar da zaman lafiya da cigaba.

Shugaban BOT na jam’iyyar PDP har ila yau ya bukaci yan Najeriya da su zauna lafiya ba tare da duba banbancin kabila, addini da na siyasa ba don samun cigaba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel