Yan bindiga sun saki DPO bayan an biya kudin fansa N3m

Yan bindiga sun saki DPO bayan an biya kudin fansa N3m

Yan bindiga sun saki wani shugaban yan sanda da suka yi garkuwa da shi a jihar Delta a karshen mako. Shugaban yan sandan mai suna Mista Okoro, shine ke jagorantar ofishin yan sandan Galilee, garin Ute-Ogbeje da ke karamar hukumar Ika North East.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an sake shi ne bayan an biya kudin fansa naira miliyan uku.

Yan bindiga ne suka yi garkuwa da jami’in dan sandan a tsakanin Onicha-Ugbo da Issele-Uku hanyar babban Turin Benin-Onitsha, bayan suyi ta harbi ba kakkautawa kafin daga bisani suka sace shi wani wuri da ba a sani ba.

An tattaro cewa an sake shi ne a ranar Lahadi bayan an ajiye kudin fansar a wani wuri.

Amma kwamishinan yan sanda, Mista Adeyinka Adeleke ya karyata lamarin.

Ya bayyana cewa abokin DPO din ne aka sace.

KU KARANTA KUMA: Wasu hazikan sojojin Najeriya sun kwanta dama yayinda Boko Haram suka kai hari bariki

Adeleke ya kuma bayyana cewa ba a biya kowani kudin fansa ba, inda ya kaddamar da cewa rundunar yan sanda ba za ta karfafa biyan kudin fansa ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel