Yanzu Yanzu: Makiyaya sun kara a Imo kan batan shanaye, mutane da dama sun jikkata

Yanzu Yanzu: Makiyaya sun kara a Imo kan batan shanaye, mutane da dama sun jikkata

Rahotanni sun kawo cewa an ji wa makiyaya da dama rauni a Agbala, karamar hukumar Owerri ta arewa a ranar Talata, 13 ga watan Agusta bayan wasu makiyaya sun yi amfani da muggan makamai a tsakaninsu biyo bayan rigima da ya kaure kan batan shanaye.

An ji wa makiyaya biyu mummunan rauni sannan anyi gaggawan daukarsu zuwa wani cibiyar lafiya na tarayya da ke Owerri.

Wata majiya tace: “Abunda ya faru shine cewa wani makiyayi ya shiga daji inda ubangidansa da shanayensa suke inda ya caki mutumin a lokacin da ya ke bacci. Sai ya kuma tafi da shanayen mutumin bayan yayi tunanin cewa ya mutu.

“Amma sai wani makiyayi wanda ke a dajin yayi gaggawan sanar da sauran makiyaya da suka zo dajin sannan suka ci karfinsa bayan sun caccake shi sau da dama sannan suka kwace shanayen da ya sace.

“Mu mazauna kauyen ne muka sanar da yan sanda. An ceto mutumin sannan aka yi gaggawan kai shi asbitin FMC da ke Owerri."

Majiyar ta kara da cewa da kyar idan mutanen biyu za su rayu, domin suna cikin wani mawuyacin hali.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan jihar Kogi ya yi babban rashi, Buhari ya aika sako zuwa gare shi

Lamarin ya haifar da cunkoso a hanyar Owerri-Aba.

Kakakin yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu, ya bayyana cewa makiyayan biyu na samun sauki a asibitin.

Ya bayyana cewa jami’an yan sandan Agbala ne suka yi gaggawan kai makiyayan asibiti bayan sun samu kira daga mutanen kauyen.

Ikeokwu ya bayyana cewa makiyayan sun samu sabani ne akan batan shanayensu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel