Gwamnan jihar Kogi ya yi babban rashi, Buhari ya aika sako zuwa gare shi

Gwamnan jihar Kogi ya yi babban rashi, Buhari ya aika sako zuwa gare shi

- Allah ya yi wa kishiyar mahaifiyar Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi rasuwa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya zuwa ga iyalan marigayiyar mai suna Madam Rekiya Momoh Bello

- Buhari ya mika sakon ta'aziyyar ne ta hannun kakakinsa Garba Shehu

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi rashi na kishiyar mahaifiyarsa, Madam Rekiya Momoh Bello.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhini akan rasuwar kishiyar mahaifiyar tasa.

A cewar wani jawabi daga Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar a ranar Talata, 13 ga watan Agusta, Buhari ya nuna bakin ciki akan mutuwar Madam Rekiya Momoh Bello, kishiyar mahaifiyar Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi.

Jawabin yace rashin ganin gwamnan a taron gwamnonin APC da aka yi a Daura tare da shugaban kasar ya ja hankalin Buhari, inda aka sanar masa da batun mutuwar Madam Rekiya, wacce jana’izarta ya sanya Gwamna Bello tsayawa a jiharsa.

Shugaban kasar yayi jaje ga iyalai, gwamnati da kuma mutanen jihar Kogi akan wannan babban rashi da suka yi.

KU KARANTA KUMA: Wasu hazikan sojojin Najeriya sun kwanta dama yayinda Boko Haram suka kai hari bariki

Jawabin ya kara da cewa shugaban kasar na yi wa marigayiyar addu’an samun rahmar Allah da kuma yiwa iyalanta fatan samun dangana da juriyar rashinta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel