Boko Haram: An yi bikin Sallah a Bama a karo na farko cikin shekaru biyar

Boko Haram: An yi bikin Sallah a Bama a karo na farko cikin shekaru biyar

Kyari Ibn Umar El-Kanemi, shehun masarautar daular Bama a jihar Borno, ya nuna farin cikinsa bisa samun damar yin bikin Sallah babba tare da mutanensa a garinsu, a karo na farko cikin shekaru biyar.

A cewar Basaraken, wannan shine karo na farko a cikin kusan shekaru biyar da al'ummar masarautar suka samu damar yin bikin Sallah a muhallinsu tare da sauran al'ummar duniya baki daya.

"Yau muna bikin Sallah a cikin kasar mu a karo na farko cikin shekaru biyar," Shehun ya bayyana cikin farinciki.

Sannan ya kara da cewa, "muna godiya ga Allah SWT da ya barmu da ran mu har muka sake ganin irin wannan rana da muka dade bamu gani ba a tarihin rayuwar mu da ta garin mu."

Bama ta kasance daya daga cikin garuruwan jihar Borno da hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram suka yi tsanani a shekarun baya, lamarin da ya tilasta mazauna garin barin gidajensu.

DUBA WANNAN: Duk wanda ya ce Buhari ba ya kokari makaryaci ne, dan wuta - Joe Igbokwe

Shi kansa, Umar El-Kanemi, sai da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da matarsa da dan sa na tsawon shekaru biyu; daga 2014 zuwa 2016.

Shi kansa basaraken tare da na wasu makwabtan sarakunan masarautu da suka hada da masarautar Dikwa karkashin mai martaba Masa II Ibn Umar El Kanemi, sun yi gudun hijira zuwa Maiduguri bayan lamuran tsaro a garuruwansu sun lalace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel