Duk wanda ya ce Buhari ba ya kokari makaryaci ne, dan wuta - Joe Ibokwe

Duk wanda ya ce Buhari ba ya kokari makaryaci ne, dan wuta - Joe Ibokwe

Sakataren yada labaran jam'iyyar APC a jihar Legas, Mista Joe Igbokwe, ya bukaci 'yan Najeriya su bawa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, goyon baya.

Ibokwe, wanda ya kasance babban bako a wani shirin gidan Talabijin na 'Channels', ya zargi jam'iyyar PDP da jefa Najeriya cikin mawuyacin hali a cikin shekaru 16 da ta yi tana mulkin Najeriya.

A cewarsa, "duk wani mai nuna alamun cewa gwamnatin shugaba Buhari ba ta yi kokari ba, makaryaci ne, dan wutar jahannama.

"Shekaru 16 PDP tayi tana mulkin Najeriya, amma babu wani abu da tayi wa jama'a duk da lokacin kasa na samun makudan kudi daga cinikin man fetur.

"Ku goyi bayan shugaban kasa, kar ku bari a yaudare ku. Duk wanda ya san yadda Najeriya ke tafi kafin zuwa Buhari, kuma yanzu ya ce Buhari ba ya kokari; makaryaci ne, dan wuta."

DUBA WANNAN: Tafiya Indiya neman magani: Zakzaky ya yada zango a Dubai

Igbokwe na wadannan kalamai ne a matsayin martani ga kalaman Ken Okolugbo, jigo a jam'iyyar PDP, wanda ya ce gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawuran da ta daukar wa 'yan Najeriya.

Jam'iyyar APC ta fara lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2015 bisa alkawarin cewa zata farfado da tattalin arzikin kasa da yakar cin hanci da rashawa.

Sai dai, jam'iyyar PDP ta dade tana zargin gwamnatin Buhari da nuna son kai da yin amfani da banbancin siyasa a yakin da take ikirarin tana yi da cin hanci da rashawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel