Buhari shugaba ne kuma abun koyi ga yan Najeriya – Inji jigon jam’iyyar adawa

Buhari shugaba ne kuma abun koyi ga yan Najeriya – Inji jigon jam’iyyar adawa

Wani jigon jam’iyyar Accord Party a jihar Oyo, Mista Saheed Ajadi, ya bayyana Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin abin koyi ga yan Najeriya duba ga yadda yake tafiyar da rayuwarsa cikin sauki kafin ya zama Shugaban kasa.

Ya bayyana hakan ne a lokacin wata hira da jaridar Vanguard a Ibadan, yayinda yake amsa tambayoyi akan mizanin da ya daura Shugaban kasar.

A cewarsa, idan har shugaban kasar zai iya kaddamar da dabbobi 150 sannan ya sanar da yan Najeriya cewa shi ba biloniya bane wanda shugabannin da suka gabata suka gaza yi, toh lallai babu shakka Buhari ya cancanci ayi koyi dashi, inda ya kara da cewa abunda ya kamata yan Najeriya suyi shine addu’an samun nasara a gare shi.

“A yanzu babu wani gwani a kasar nan. Babban matsala ne. Buhari gwani ne. Idan har Shugaban kasarmu zai iya kaddamar da dabbobi 150 sannan ya fada ma Yan Najeriya cewa shi ba biloniya bane sannan ba za mu iya bayar da shaida kan shugabannin da suka gabata ba, toh lallai Buhari ya cancanci ayi koyi da shi.

“Kawai abunda muke bukata shine yi masa addu’an samun nasara da kuma aiki tare da shi. Ina son Buhari; ina son shi saboda ya kamata ace ka zamo mai son kasar idan har kai dan Najeriya ne.

KU KARANTA KUMA: Duk da sabanin da ke tsakaninsu: Obaseki ya kai wa Oshiomhole ziyarar bazata

“Ina son Buhari a matsayinsa na Shugaban kasa na. Zancen gaskiya, ina da muradin yin aiki da Shugaban kasar a kyauta domin ganin ya cimma nasara; ni ba dan APC ane, kuma bana ra’ayin APC," inji Ajadi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel