Duk da sabanin da ke tsakaninsu: Obaseki ya kai wa Oshiomhole ziyarar bazata

Duk da sabanin da ke tsakaninsu: Obaseki ya kai wa Oshiomhole ziyarar bazata

- Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya kai wa Adams Oshiomhole ziyarar bazata

- Obaseki ya kai masa ziyarar ne duk da rahotannin sabanin da ke tsakaninsu

- Gwamnan ya nuna godiyarsa akan goyon bayan da ya samu daga al’umman Musulmi yayinda yake jadadda jajircewarsa na kawo ci gaba a jihar

Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo, a ranar Litinin, 12 ga watan Agusta, ya kai wa Adams Oshiomhole ziyarar bazata duk da rahotannin sabanin da ke tsakaninsu.

Obaseki ya ziyar Oshiomhole, wanda ke tare da mahaifiyarsa, Aishetu Oshiomhole, domin hutun babban Sallah, a mahaifarsa ta Iyamho.

An tattaro cewa gwamnan ya nuna godiyarsa akan goyon bayan da ya samu daga al’umman Musulmi yayinda yake jadadda jajircewarsa na kawo ci gaba a jihar.

A nashi bangaren, Oshiomhole ya yaba ma gwamnan akan tsarin shugabancinsa sannan ya shawarce shi da kada ya bi hanyar bata da ke kokarin kawo rabuwar kai a jihar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: El-Zakzaky da matarsa sun isa Indiya, za a fara basu kulawa ba tare da bata lokaci ba (hotuna)

Da yake jawai bayan ganawar, Crusoe Osagie, hadimin gwamnan a kafofin labarai, ya yaba ma tsarin shugabanci na Obaseki.

Ya bayyana cewa wasu mutane ne ke rura wutar rikicin tsakanin Obaseki da Oshiomhole domin su haddasa tashin hankali da rabuwar kai a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel