Kisan yan sanda: Kwamitin bincike ya kama sojoji 5 da jami’an yan sanda 2 a Taraba

Kisan yan sanda: Kwamitin bincike ya kama sojoji 5 da jami’an yan sanda 2 a Taraba

Rahotanni sun kawo cewa kwamitin da ke bincike kan kisan jami’an yan sanda uku da wani dan farin hula a ranar 6 ga watan Agusta a bakin aiki sun kama jami’an yan sanda biyu da ke aiki a yankin Ibi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kama jami’an yan sandan biyu bisa zargin yi tsegumi ga gawurtaccen mai garkuwa da mutane Hamisu Wadume akan shirin kama shi.

An tattaro cewa an dauki jami’an yan sandan zuwa babbar birnin tarayya Abuja.

An kuma rahoto cewa kwamitin ya yi umurnin kama sojoji biyar, wadanda ke bakin aiki a tashar bincike na rundunar sojoji.

Majiyarmu ta ci gaba da cewa an wargaza tashohin bincike na sojoji guda biyu a tsakanin iyakar kananan hukumomin Wukari da Ibi.

Rahoto ya kawo cewa an dauki gawawwakin jami’an yan sandan uku da dan farin hular daga Jalingo zuwa Abuja.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen Hakiman da sarkin Gaya ya dakatar saboda ci gaba da yi wa sarkin Kano mubaya'a

Daily Trust ta kuma kawo cewa mutane 60 da ake zargi da yi wa madugun mai garkuwa da mutanen, Hamisu Wadume aiki sun ci kafar kare.

A halin yanzu, wata majiya ta rahoto cewa tawagar mataimakin kwamishinan yan sanda Abba Kyari, sun rufe wasu daga cikin gidaje mallakar madugun mai garkuwa da mutanen a Ibi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel