Tafiya Indiya neman magani: Zakzaky ya yada zango a Dubai

Tafiya Indiya neman magani: Zakzaky ya yada zango a Dubai

Shugaban kungiyar 'yan uwa Musulmi (IMN), wacce aka fi kira da Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya yada zango a kasar Dubai a hanyarsa ta zuwa kasar Indiya neman magani.

A wata hira da gidan Talabijin na 'Channels', kakakin kungiyar IMN ya bayyana cewa Zakzaky da matarsa, Zeenat, sun sauka a filin jiragen sama na kasar Dubai da misalin karfe 4:00 na safiyar ranar Litinin.

Ana sa ran cewa Zakzaky da matarsa zasu cigaba da bulaguronsu zuwa kasar Indiya, kuma ana sa ran zasu sauka a kasar Indiya da misalin karfe 2:30 na rana, lokacin Najeriya.

Zakzaky da matarsa tare da jami'an tsaron Najeriya sun bar Najeriya ne zuwa kasar Indiya a jirgin kamfanain 'Emirate' mai lamba kamar haka: EK2614.

Zeenat da Zakzaky sun isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da duku-dukun safiyar ranar Litin domin tashi zuwa asibitin 'Medanta' na kasar Indiya, inda za a duba lafiyarsu, kamar yadda lauyoyinsu suka bukata.

DUBA WANNAN: Abu 5 da ya kamata ku sani a kan asibitin da za a kai Zakzaky a kasar Indiya

Wata babbar kotun jihar Kaduna ce ta bayar da belin Zakzaky da Zeenat domin su fita zuwa kasar Indiya a duba lafiyarsu, bayan lauyoyinsu sun sanar da kotun cewa lafiyarsu na fuskantar barazana daga cututtuka daban-daban.

Babban lauya, Femi Falana, ne ya rubuta takardar neman kotun ta bayar da belin Zakzaky da Zeenat domin a duba lafiyarsu, sakamakon tabarbarewar da ta yi saboda tsare su da gwamnati ta yi tun shekarar 2015.

Kotun ta sahalewa Zakzaky da matarsa fita kasar Indiya bisa rakiyar jami'an tsaro da kuma wakilan gwamnati, wadanda ake sa ran zasu saka ido a kansu, sannan su sako su a gaba su dawo Najeriya da zarar an sallame su daga asibiti domin a cigaba da shari'ar da gwamnati ke yi da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel