Kisan yan sanda da sojoji suka yi: Buhari na jiran sakamakon bincike – Garba Shehu

Kisan yan sanda da sojoji suka yi: Buhari na jiran sakamakon bincike – Garba Shehu

- Hadimin Shugaban kasa, Garba Shehu yace hedikwatan hukumar tsaro na gudanar da bincike akan kisan yan sanda uku da dan farin hula daya da sojoji suka yi a jihar Taraba

- Garba Shehu yayi watsi da cece-kucen dake cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana nuna bambanci game da lamarin

- Hadimin Shugaban kasar yace Buhari na bin tsari ne kafin daukan mataki akan lamarin

Wani kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jiran sakamakon binciken da hedikwatan tsaro ke gabatarwa akan lamarin kisan yan sanda uku da dan farin hula daya da sojoji suka yi a jihar Taraba kafin daukan mataki akan lamarin.

Garba Shehu wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 12 ga watan Agusta, har ila yau yayi watsi da cece-kucen da ke cewa Shugaban kasar na nuna banbanci akan lamarin.

Hadimin shugaban kasar yace Buhari ya bada umurni ga shugaban ma’aikatun tsaro da ya kafa kwamitin bincike dauke da wakilai daga dukkanin hukumomin tsaron kasar, hade da hukumar yan sanda domin su yi bincike lamarin da ya kai ga kisan yan sandan.

Haka zalika, an kama jami’in rundunan sojin da ya bada umurnin kisan yan sandan da dan farin hula wadanda suka kasance masu jigilan wani shahararren mai garkuwa da mutane mai suna Hamisu Bala Wadume.

KU KARANTA KUMA: Hajjin bana: Najeriya ta rasa mahajjata 9 a kasar Saudiyya

Vanguard ta rahoto cewa an kama jami’in a ranar Lahadi, 11 ga watan Agusta, bayan kwamitin ta gayyace shi don amsa tambayoyi, ya kuma kasance mai rike da mukamin Kyaftin.

Wani majiyi a rundunar soji yace wassu sojojin sun kubutar da mai garkuwa da mutane a hanyar Ibi-Wukari. Har ila yau an tattaro cewa Kyaftin din ya bada umurni ga sojojin da su harbi motar dake Jigilar Wadume da kuma umurnin cewa kada a bar ko daya daga cikin yan sandan da rai yayin da dan fashin ke tserewa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel