Yaki da ta'addanci: Buratai ya yabi sadaukarwar dakarun sojin Najeriya

Yaki da ta'addanci: Buratai ya yabi sadaukarwar dakarun sojin Najeriya

Shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, ya yi alhinin tunawa da dakarun sojin Najeriya wadanda suka kwanta dama da kuma wadanda suka riga mu gidan gaskiya a yayin kare martabar kasar nan a filin daga.

Ya kuma yabi dakarun sojin kasar nan da ke ci gaba da tsayuwar daka wajen fuskantar kalubale na rashin tsaro da suka yiwa kasar nan dabaibayi.

A cewar kakakin rundunar sojin kasan Najeriya, Kanal Sagir Musa, shugaban hafsin sojin ya ribaci lokacin bikin sallah babba wajen gabatar da sakonnin sa na taya murna ga dakarun sojin tare da yabawa gwarzontakar su ta sadaukar da kai duk da kalubalen da suke fuskanta.

Kanal Musa ya ce Buratai wanda ya gudanar da bikin babbar sallah tare da dakarun sojin filin daga, ya nemi da su kara hobbasa wajen tabbatar da kare martabar kasar domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma.

Ya ci gaba da cewa, shugaban hafsin sojin wanda jagoran horas da dakaru ya wakilta, ya kuma ziyarci dakarun soji da ke jinya a cibiyar lafiya ta dakaru ta barikin sojin Maimalari a birnin Maiduguri na jihar Borno.

KARANTA KUMA: Sanwo-Olu ya fidda sunayen 'yan majalisar gwamnatin Legas

Ya kara da cewa, sabanin kalubale da ta ke ci gaba da fuskanta babu zato babu tsammani, hukumar dakarun sojin kasa na ci gaba da yin iyaka bakin kokarinta wajen kare martabar kasar nan gwargwadon iko na tabbatar da muradin al'ummar kasa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel