Sanwo-Olu ya fidda sunayen 'yan majalisar gwamnatin Legas

Sanwo-Olu ya fidda sunayen 'yan majalisar gwamnatin Legas

A ranar Talata 13 ga watan Agustan 2019, gwamnan jihar Legas, babajide Sanwo-Olu, ya aike da kason karshe na jerin sunayen 'yan majalisar gwamnatinsa zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa.

Wannan lamari ya zo ne bayan makonni hudu da gwamnan ya aike da kason farkon na zababbun 'yan majalisarsa da suka hadar da mashawarta da kuma kwamishinoni zuwa majalisar dokokin jihar kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kwamishinoni da kuma mashawarta na musamman guda 13 sun samu shiga cikin kashin karshe da gwamnan ya aike da sunayensu zuwa majalisar dokokin jihar Legas.

Cikin sanarwar da babban sakataren sadarwa da yada labarai na fadar gwamnatin Legas ya gabata, Gboyega Akosile ya ce wannan kashi na karshe ya kunshi sunayen gogaggun 'yan siyasa da suka fahimci duk wani kwararo da sako na bukatun jihar da kuma fahimtar akidar ci gaba da gwamnan jihar.

Ga kashi na biyu na jerin sunayen mutane 13 da suka samu shiga cikin sahun 'yan majalisar zantarwa na gwamnatin Legas kamar haka:

1. Oladele Ajayi

2. Oluwatoyin Fayinka

3. Yetunde Arobieke

4. Olarenwaju Sanusi

5. Joe Igbokwe

6. Bonu Solomon Saanu

7. Kabiru Ahmed

8. Lolas Akande

9. Prince AnofiI Olarenwaju Elegushi

KARANTA KUMA: Buhari ya taya Alhazan Najeriya murnar kammala aikin Hajji

10. Solape Hammond

11. Moruf Akinderu Fatai

12. Shulamite Oufunke Adebolu

13. Tokunbo Waha

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel