Buhari ya taya Alhazan Najeriya murnar kammala aikin Hajji

Buhari ya taya Alhazan Najeriya murnar kammala aikin Hajji

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Alhazan Najeriya murnar bikin babbar sallah da kuma ta kammala aikin hajjin bana a kasa mai tsarki.

Shugaban kasar ya kuma yi alhini tare da jajantawa 'yan uwa, gwamnati, Alhazai, da kuma ma'aikatan hukumar jin dadin Alhazai dangane da rasuwar wasu daga cikin mahajjatan kasar nan da suka riga mu gidan gaskiya a kasar Saudiya.

Hukumar jin dadin Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta bayyana cewa a bana musulmin kasar 45,000 ne suka gudanar da aikin hajjin bana a kasar Saudiyya. Hukumar ta bayyana cewa 'yan Najeriya 9 ne suka riga gidan gaskiya gabani da kuma bayan kammala aikin hajjin.

Shugaban hukumar NAHCON na kasa, Alhaji Abdullahi Muhammad, shi ne ya wakilci shugaban kasa Buhari a taron ranara Litinin da aka gudanar cikin birnin Mina dake kasar Saudiya.

Buhari ya kirayi mahajjatan Najeriya da su tsananta gudanar da addu'o'i a kan Najeriya na neman magance kalubalen da take fuskanta kama daga tabarbarewar tattalin arziki, rashin tsaro gami da tsananin adawa ta siyasa.

KARANTA KUMA: Direba ya kashe dan Adaidaita Sahun da ya gogar masa mota a Legas

Cikin zayyana nasa jawaban, shugaban hukumar jin dadin Alhazai na jihar Kano, Shaykh Abdullahi Pakistan da kuma sakatarensa, Muhammad Danbatta, sun bayyana gamsuwar su a kan kwazon da hukumar NAHCON ta yi yayin dawainiyarta a aikin hajjin na bana.

Sun yabawa hukumar NAHCON musamman dangane da yadda ta tabbatar da biyan bukatu da kuma muradin Alhazan Kano a bangaren jigila, masauki da kuma sauran ababe yayin aikin hajjin a bana.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel